Connect with us

Labarai

Shugaba Tinubu ya amince da yin ayyukan tituna 27

Published

on

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya amince da gudanar da ayyukan tituna guda 27 da darajarsu ta haura tiriliyan uku da biliyan dari Tara a wani mataki na inganta hanyoyi a sassan ƙasar nan.

 

Ministan Ayyuka, David Umahi, ne ya bayyana hakan bayan taron Majalisar Zartarwa ta kasa da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. 

 

Ya ce ayyukan za su gudana a jihohin Adamawa, Benue, Cross River, Ebonyi, Ekiti, Kogi, Kwara, Lagos, Niger, Ondo, Osun, Oyo, Plateau, Taraba da Yobe.

 

Umahi ya ce majalisar ta kuma amince da sake bai wa Aliko Dangote kwangilar aikin titi mai nisan kilomita 409 a Jihar Niger, ƙarƙashin tsarin Tax Credit Scheme, kan kuɗi naira tiriliyan daya da biliyan dari Takwas.

 

Sauran manyan ayyukan da aka amince da su sun haɗa da ninka titin Ilorin–Ogbomoso kan biliyan N276, sake gina titin Iseyin–Eruwa–Agbesi da ya haɗa jihohin Oyo da Kwara kan biliyan N265, da kuma ninka tsohon titin Ijaye zuwa Ilorin tare da reshe zuwa Akinmorin kan biliyan N217. 

 

Haka kuma an ware biliyan N116 domin aikin titin Abakaliki–Afikpo mai tsawon kilomita 21 a Jihar Ebonyi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!