Labarai
Shugaba Tinubu ya naɗa Gbajabiamila shugaban kwamitin kafa yan sandan jihohi

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya naɗa shugaban ma’aikatan fadarsa Femi Gbajabiamila, a matsayin shugaban kwamitin kafa ‘yan sandan jihohi.
Wannan na cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasar shawara kan harkokin yaɗa labarai Bayo Onanuga, ya fitar, yana mai cewa, babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi shi mamba ne a kwamitin.
Ta cikin sanarwar, Onanuga ya ce an kafa wannan kwamiti ne domin shirya tsarin doka da zai ba da damar aiwatar da tsarin kafa ‘yan sandan jihohi a faɗin Najeriya.
Shugaba Tinubu, wanda Gbajabiamila ya wakilta a wajen ƙaddamar da kwamitin a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, ya bayyana cewa kafa kwamitin ya zama wajibi ne bayan Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta amince da Kudirin Gyaran Kundin Tsarin Mulki na shekarar 2026 da ya tanadi kafa ‘yan sandan jihohi.
You must be logged in to post a comment Login