Connect with us

Labarai

Farashin ɗanyen mai ya ƙaru bayan soke yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran

Published

on

Farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya ƙaru da sama da kashi biyar cikin 100, bayan da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran ta rushe.

 

Bayan kalaman Trump, farashin ɗanyen mai na Brent, wanda ake amfani da shi a matsayin ma’aunin kasuwar mai ta duniya, ya tashi zuwa dala 78.09 kan kowace ganga.

 

Rahotanni sun nuna cewa masu zuba jari na sa ido sosai kan yadda rikici tsakanin ƙasashen biyu ke ƙara taɓarɓarewa.

 

Tun kafin wannan sanarwa, farashin mai ya fara nuna alamun tashin gwauron zabi sakamakon musayar hare-haren da Amurka da Iran suka yi wa juna, musamman bayan hare-haren da aka kai kan tankokin dakon mai a mashigar Hormuz.

 

Masana tattalin arziki na gargaɗin cewa idan rikicin ya ci gaba da tsananta, hakan na iya ƙara dagula kasuwannin makamashi na duniya tare da haifar da ƙarin hauhawar farashin mai a kwanaki masu zuwa.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!