Connect with us

Labarai

SDP ta soki Tinubu kan naɗa Gbajabiamila shugaban kwamitin tsara dokar kafa yan sandan jihohi

Published

on

Jam’iyyar SDP ta soki matakin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na naɗa Shugaban Ma’aikatansa, Femi Gbajabiamila, a matsayin shugaban kwamitin da zai tsara dokar aiwatar da kafa yan sandan jihohi.

 

Shugaban SDP na ƙasa, Farfesa Sadiq Gombe, ya ce bai dace Gbajabiamila ya ci gaba da riƙe wannan muƙami ba, kasancewar ana binciken wasu zarge-zarge da ake masa.

 

Ya ce ya kamata ya ajiye muƙaminsa har sai an kammala binciken domin tabbatar da gaskiya.

 

Sai dai Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta zarge-zargen da ake yi wa Gbajabiamila, yayin da Shugaba Tinubu ya bayyana cewa yana da cikakken yaƙini da amincinsa, tare da ci gaba da ba shi goyon baya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!