Ƙetare
Shugaba Trump zai ƙarfafa dokokin zaɓe a Amurka

Shugaban Amurka Trump ya ce zai kauce wa Majalisar Dokoki tare da tilasta sabbin dokoki masu tsauri na tantance masu kaɗa ƙuri’a kafin zaɓen tsakiyar wa’adi na watan Nuwamba.
Majalisar ta amince da wani ƙudiri da ke buƙatar masu son kaɗa ƙuri’a su gabatar da shaidar zama ƴan ƙasa, amma da wuya ya samu karɓuwa a Majalisar Dattawa.
Mista Trump bai yi bayanin yadda zai sanya irin waɗannan dokoki ba, waɗanda masu suka ke cewa za su hana miliyoyin masu kaɗa ƙuri’a shiga zaɓen.
Sai dai ya sha iƙirarin cewa magudin zaɓe ya zama ruwan dare a Amurka, ba tare da gabatar da wata shaida ba.
You must be logged in to post a comment Login