Ƙetare
Shugaba William Ruto ya bukaci kasashe Afrika masu karfin masana’antu su samar da karin fasahohi
Shugaban kasar Kenya William Ruto, ya ce, ya kamata manyan kasashe masu karfin masana’antu, su samar da kudi da fasahohin da ake bukata wajen taimakawa kasashen Afrika domin shawo kan matsalolin da sauyin yanayi ke haifarwa.
Da yake jawabi yayin taron makon tattauna muhimman batutuwan nahiyar Afrika na bana, wanda ake kira da Ibrahim Governance Weekend, da ke gudana yanzu haka a Nairobi babban birnin kasar ta Kenya, Shugaba William Ruto, ya jaddada cewa manyan kasashe na da nauyin da ya rataya a wuyansu na tabbatar da adalci wajen shawo kan sauyin yanayi a Afrika.
Haka kuma ya kara da cewa, karuwar yanayin zafi ne ke yin matukar tasiri a kan muhalli da rayuwar jama’a.
Ya kara da cewa nahiyar Afrika na bukatar diyyar asarar da ta tafka saboda matsalolin da sauyin yanayi ya haifar kan tattalin arzikinta.
Shugaban kasar ta Kenya, ya ce, ya kamata a taimaka wa Afrika wajen sake farfado da tsarin kiyaye muhalli, yana mai cewa, Kenya za ta karbi bakuncin taron nahiyar kan sauyin yanayi daga ranar 4 zuwa 6 ga watan Satumban bana.
You must be logged in to post a comment Login