Labarai
Shugaban Buhari ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan Sheikh Ibrahim Ibn Saleh Al-Hussaini
Shugaban kasa Muhamadu Buhari ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan Sheikh Ibrahim Ibn Saleh Al-Hussaini, shugaban kwamitin Fatwa na kwamitin koli na addinin musulunci, wanda aka fi sani da Shaykh Sharif Saleh, kan rasuwar babban dansa Alhaji Musa Alkasim.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya fitar, Shugaba Buhari ya aike da sakon ta’aziyarsa ga shehin malamin da gwamnati da kuma ilahirin al’umma jihar Borno, kan rasuwar Alhaji Musa Alkasim.
Shugaban kasa Buhari ya ce ya kadu da jin labarin rasuwar Alhaji Musa wanda ya bayyana a matsayin wata majingina ga shehin malamin.
Buhari ya bayyana marigayi Alhaji Musa Alkasim mai shekara 59 a matsayin mutum mai halin dattako wanda za a dade ba manta da shi ba.
Shugaba Buhari, ya kuma yi addu’ar neman gafara a gare shi, tare da bai wa iyalansa da al’ummar Borno hakurin jure rashinsa.
You must be logged in to post a comment Login