Kiwon Lafiya
Shugaban hukumar hana fasakauri ya ce masu kokawa ga gwamnatin Buhari ragwaye ne
Shugaban hukumar hana fasakauri ta kasa wato Kwastam kanal Hameed Ali mai ritaya ya ce mafi akasarin ‘yan Najeriya da ke kukan yunwa a karkashin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ragwaye ne, da basu da karfin zuciyar tashi domin neman na kansu.
Shugaban na Kwastam ya bayyana haka ne, yayin da ya ke karin haske dangane da nasarorin shirin gwamnatin tarayya kan bunkasa ayyukan noma a kasar nan, a wata ganawa da yayi da kungiyar magoya bayan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a fadar gwamnati da ke Abuja.
A cewar Hameed Ali, babu yadda za ayi abinci ya rika fadowa mutane daga sama, dan haka ya zama tilas mutane su tashi tsaye domin amfani da damar su wajen neman abin rufawa kai asiri.
Dangane da shugabancin Buhari kuwa, shugaban na kwastam ya ce kaunar Najeriya da ‘yan kasar ne ya sanya shi fafutukar karbar jagorancin kasar duk da cewa shekarun sa sun haura 70.
Ali ya kara da cewa inda shi ne ya ke da yawan shekarun shugaba Buhari, ga fansho mai kyau da gidan sa na zama a Daura, ba zai dorawa kan sa nauyin da zai hanashi sararawa ba ta hanyar shiga siyasa, amma kaunar kasar sa ta sa shugaba Buhari yanke wannan shawara.