Labarai
Kotu ce za ta yanke hukunci kan cancantar yan takarar da aka cire sunayensu- INEC

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya INEC, ta ce, kotu ce, za ta yanke hukunci na ƙarshe kan cancantar ’yan takarar da aka cire sunayensu daga na waɗanda za su fafata a zaɓen gwamnonin jihohi da na ’yan majalisun jihohi na shekarar 2027.
Hukumar ta kuma bai wa jam’iyyun siyasa da ’yan takarar da abin ya shafa wa’adin kwanaki 14 domin shigar da ƙorafe-ƙorafe, idan suna neman a yi musu adalci.
Kwamishinan INEC kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe, Mohammed Haruna, ne ya bayyana hakan ya na mai cewa ba hukumar ce ta hana ’yan takarar shiga zaɓen ba.
A cewarsa, jam’iyyun siyasar ne suka gaza cika wasu ƙa’idojin da kundin tsarin mulki ya tanada.
Ya ƙara da cewa hakan ya yi daidai da hukuncin Kotun Ƙoli, wanda ya umarci jam’iyyun siyasa su gabatar da rajistar mambobinsu da ta ƙunshi sunayen ’yan takarar da suka tsayar.
You must be logged in to post a comment Login