Labarai
Shugaban majalisar Yobe ya sha kaye bayan ya shafe shekaru 20 a majalisa
Shugaban majalisar dokokin jihar Yobe Ahmed Lawan Mirwa na jam’iyyar APC mai mulki ya rasa kujerarsa a zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jihar da aka kammala jiya Asabar.
Lawan Mirwa wanda ke wakiltar karamar hukumar Nguru a majalisar dokokin jihar Yobe tun daga shekarar 2003, ya sha kaye a hannun matashin dan takarar jam’iyyar PDP Musa Lawan Majakura.
Rahotanni sun nuna cewa Musa Lawan Majakura na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u dubu 6 da 648, inda ya doke Ahmed Lawan Mirwa din wanda ya samu kuri’u dubu 6 da 466.
Bukar Jatau na jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 23, yayin da Mai Zare Idriss Idriss na jam’iyyar APM ya samu kuri’u 14 sai Isah Sa’idu Shehu na jam’iyyar ADC ya samu kuri’u 30.
Wannan shi ne sakamakon zaben, kamar yadda jami’in dake tattara sakamakon na karamar hukumar ta Nguru Alhaji Mahdi Damatu ya bayyana.
You must be logged in to post a comment Login