Labaran Kano
Shugabanni sun rinka sara-suna-duban-gatari- Shu’aibu Aliyu
Mai fashin baki kan al’amuran yau da kullum, Alhaji Shu’aibu Aliyu, ya ce, shugabanci na bukatar, shugaba ya rinka sara -yana-dubar-bakin-gatari, ta yadda zai samu damar yiwa al’ummar da ya ke mulka adalci a bangarori daban-daban.
Alhaji Shuaibu ya ce, sai shugabanni sun rike gaskiya da daukar shawarwari da hakuri da al’umma tare da toshe duk wata kafar barna a cikin jama’a, sannan za a samu daidaito a shugabanci.
Mai fashin Bakin Alhaji Shuaibu Aliyu ya bayyana hakan ne a cikin shirin Duniyar Mu A Yau na jiya da gidan Freedom Radio ya saba kowa a duk ranakun Litinin zuwa Alhamis wanda na jiyan ya maida hankali kan kyakyawan shugabanci.
Alhaji Shua’ibu, ya ce, kafin zuwan kafafen sada zumunta na Internet, al’umma na girmama na gaba da su da kuma wadanda su ke shugabantarsu tare da yin biyayya kan hukuncin da manya ko shugabanni su ka yanke.
Ya kuma ce, zuwan shafukan sada zumunta na zamani sun sauya yayin zamantakewar al’umma musamman a kasar nan ta fannin rashin ganin girmama manya da kuma raina shugabanni.
A nasa bangaran shugaban sashen nazarin ilimin zamantakewa, ya ce, ya kamata kungiyoyin da ke rajin kawo ci gaba da kuma kare hakkin al’umma da su rinka kokari wajan wayar da kan Jama’a, musamman kan yadda shugabanni ke tafiyar da mulki ga alummar a fadin kasar nan.
Mai fashin bakin ya kara da cewae, hakan zai baiwa jama’a damar bibiyar yadda shugabanni ke tafikar da alamuran mulki, idan ya yi kuskure to yakamata a ganar dashi gaskiya don ya gyara, idan kuma ya yi daidai to ayaba masa.
Bakin sun ce, tarbiya da halaye ma su kyau ke sa a kira mutum da sunan Dattijo wanda ke da kishin addini da al’umma da kuma kasar sa ta hanyar tsayawa kan gaskiya komai dacin ta.
You must be logged in to post a comment Login