Connect with us

Labarai

Shugabannin Kafafen yaɗa labaran Kano sun yi Allah-wadai da farmakar yan jarida yayin dawowa daga taron APC

Published

on

Ƙungiyar Shugabannin Kafofin Yaɗa Labarai ta Kano ta yi Allah-wadai da harin da aka kai wa wasu ’yan jarida da ke dawowa daga gangamin jam’iyyar APC a Kano ranar Asabar 5 ga Satumba 2026.

 

A cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Ado Saidu Warawa, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta ce wasu ’yan jarida sun fuskanci hari a yankin Kofar Nassarawa, inda ake zargin wasu ’yan daba da fasa gilashin motar Radio Nigeria Pyramid FM da ke ɗauke da ’yan jarida da jami’an tsaro.

 

Ƙungiyar ta buƙaci gwamnatin jihar Kano da rundunar ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro su gudanar da bincike cikin gaggawa, tare da gano waɗanda suka kai harin da kuma gurfanar da su a gaban shari’a.

 

Ta kuma yi kira ga jam’iyyun siyasa da magoya bayansu da su mutunta aikin ’yan jarida, tana mai cewa ’yan jarida ba abokan gaba ko abokan hamayyar siyasa ba ne, illa ƙwararru da ke gudanar da aikin da ya shafi amfanin jama’a.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!