Connect with us

Labarai

An fara shirin nada sabon Sarkin Gumel

Published

on

A yau Litinin ake sa ran yin bikin nadin sabon Sarkin Gumel Dr. Lawan Ahmad Muhammad Sani tare da karbar gaisuwar jaddada goyon bayan baya daga ‘yan majalisar sarki da sauran Hakiman masarautar.

 

Sabon Sarkin mai shekaru 55 da haihuwa ya kasance babban ‘da a gurin marigayi sarkin Gumel na 16 Dr. Ahmad Muhammad Sani II, wadda ya shafe shekaru 46 yana mulkin masarautar kafin rasuwarsa kwanaki hudu da suka gabata Kairon kasar Egypt.

 

A jiya ne dai sakataran gwamnatin jihar Jigawa Malam Bala Ibrahim ya mikawa sabon Sarkin Takardar amincewar nadin a madadin gwamnatin jihar bayan bin duk wasu matakan dokokin nada sarki a jihar.

Da yake jawabi jim kadan bayan mika takardar mai Martaba sarkin Hadejia kana shugaban majalisar sarakunan jihar Jigawa Alhaji Adamu Abubakar Maje CON, bayan taya sarkin murna ya kuma yi masa nasihar rike gaskiya da amanar jama’a kamar yadda mahaifinsa ya gudanar cikin shekaru 46.

 

Haka kuma, ya bukaci al’ummar masarautar dasu kasance masu bashi hadin kai da yi masa biyayya da addu’ar samun nasara da shawarwari masu kyau.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!