Labarai
Iyalan tsoffin Yan sanda sun yi zanga-zanga kan rushe musu muhallai a Sokoto

Wasu iyalan jami’an ’yan sanda sun gudanar da zanga-zanga a Sokoto, bayan da aka rushe wasu gidajensu da ke kan titin Kontagora.
Guda cikin matayen da aka sakaye sunanta ta ce rushewar ta yi wa iyalan jami’an da suka sadaukar da rayukansu wajen kare kasa rashin adalci, inda ta nemi hukumomin ’yan sanda su shiga tsakani.
Sai dai Kwamishinan Filaye da Gidaje na jihar, Nasiru Dantsoho, ya ce bai da masaniya kan rushewar, yana mai cewa batun yana gaban kotu.
Rahotanni sun ce kotu ta umurci wadanda abin ya shafa da su bayyana gabanta ranar Talata, 8 ga Satumba, 2026.
You must be logged in to post a comment Login