Labarai
ShugabaTinubu ya nuna farin ciki kan ceto ɗalibai da malaman Jihar Oyo

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya nuna farin ciki kan ceto ɗalibai da malamai da aka sace daga makarantu a ƙaramar hukumar Oriire da ke Jihar Oyo, bayan sun shafe kwanaki 56 a hannun masu garkuwa.
A cikin wata sanarwa da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a jiya Juma’a, Tinubu ya yaba wa rundunar soji, Hukumar Tsaro ta DSS da Rundunar ‘Yan Sanda bisa haɗin gwiwar da suka yi wajen gudanar da aikin ceton cikin nasara ba tare da rasa rayuka ba.
Shugaban Ƙasar ya kuma jinjinawa jami’an tsaron bisa cafke mutane takwas da ake zargi da hannu a satar, tare da kashe wasu daga cikin masu garkuwar yayin aikin.
Tinubu ya bayyana cewa nasarar ceton ta kawo babban sauƙi ga iyalan waɗanda abin ya shafa da kuma al’ummar Najeriya baki ɗaya.
Ya ce yana matuƙar farin ciki da yadda jami’an tsaro suka gudanar da aikin cikin ƙwarewa, tare da jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
You must be logged in to post a comment Login