Connect with us

Labarai

Gwamna Fubara na shirin gabatar da kasafin kuɗin bana

Published

on

Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, na shirin gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 ga Majalisar Dokokin jihar a yau Juma’a, bayan da majalisar ta amince da tsarin Kashe Kuɗaɗe na matsakaicin lokaci na shekarun 2026 zuwa 2027 da ya gabatar a makon da ya gabata.

Ana sa ran gwamnan zai gabatar da kasafin ne a zauren da ‘yan majalisar ke amfani da shi a halin yanzu da ke Assembly Quarters, sakamakon lalacewar ginin majalisar yayin rikicin siyasar jihar a shekaru uku da suka gabata.

Wata majiya daga Gidan Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa an kammala duk shirye-shiryen gabatar da kasafin, tana mai cewa yau ce ranar da ake jira domin gwamnan ya gabatar da kudirin kasafin.

An jinkirta gabatar da kasafin ne sakamakon rikicin siyasa tsakanin Gwamna Fubara da Majalisar Dokokin jihar ƙarƙashin jagorancin Martin Amaewhule.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!