Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Siyasar kabilanci da addini ta janyo koma baya a zaben bana- ACF

Published

on

Kungiyar tuntuba ta Arewa Consultative Forum ta yi zargin cewa siyasar kabilanci da bambancin addini da wasu suka nuna a zabukan da aka kammala a baya-bayan nan, sun taimaka wajen haddasa rashin fitowar mutane domin yin zaben.

Sakatare janar na kungiyar Murtala Aliyu ne ya bayyana hakan, ta cikin wata sanarwa da ya fitar mai taken magance matalolin da aka fuskanta yayin zabe, don kaucewa sake afkuwarsu a nan gaba.

Sanarwar ta jinjinawa wadanda suka garzaya Kotu domin neman hakkokin da suka ce an tauye musu yayin zaben, maimakon su bi wata hanya da ka iya janyo wa kasar matsala.

Murtala Aliyu ya kara da cewa matukar ba a hanzarta kawar da wannan matsala ta bangaranci da bambancin addini a cikin siyasar kasar nan ba, to hakika tamkar an fara gini ne da tubalin toka.

Rahoton: Abdulkarim Muhammad Abdulkarim

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!