Labaran Kano
Siyasar Kano: Dalilan korar Kwankwaso daga PDP
Jam’iyyar PDP tsagin Alhaji Aminu Wali ta bayyana dalilan da suka sanya ta dakatar da tsohon gwamnan Kano Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso daga jam’iyyar.
Shugaban jam’iyyar Munhaminna Baƙo Lamiɗo shi ne ya sanar da korar Kwankwaso da ranar Alhamis bayan babban taron jam’iyyar na jiha.
Lamiɗo ya ce, an dakatar da shi ne saboda zargin yiwa jam’iyyar zagon ƙasa, da kuma haɗa baki da jam’iyya mai ci a matakin ƙasa don samun takara a 2023.
Haka kuma Kwankwason ya haifar da baƙin jini da ƙiyayya a tsakanin ƴan jam’iyyar PDP wanda ya haifar da asarar ɗan majalisar tarayya Ali Datti Yako.
Labarai masu alaka:
Siyasar Kano: An ja layi tsakanin Sha’aban da Ganduje
Siyasar Kano: Ko Baffa Bichi ya ƙwace takarar Abba Gida-Gida?
Lamiɗo ya ƙara da cewa, Kwankwason na karya dokokin jam’iyyar tare da ƙin biyayya ga kwamitin zartarwa na jam’iyyar a Kano.
Abu na ƙarshe ya ce, Kwankwaso yana cin zarafi tare da wulaƙanta shugabannin jam’iyyar na jiha.
Har kawo lokacin haɗa wannan rahoto, jam’iyyar PDP tsagin Kwankwason ba ta ce komai ba game da batun.
You must be logged in to post a comment Login