Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Siyasar Kano: PDP ta gargaɗi Ganduje kan cefanar da kadarorin gwamnati

Published

on

Jam’iyyar PDP ta gargaɗi gwamnatin Kano kan sayar da kadarorin gwamnati.

Ɗaya daga jagororin jam’iyyar na Kano Kwamaret Aminu Abdussalam ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai da jam’iyyar ta kira.

Kwamaret Abdussalam ya ce, abin takaici ne yadda gwamnatin Kano ke cefanar da wuraren al’ummar Kano masu don biyan buƙatar kai.

A cewarsa, in har jam’iyyar PDP ta yi nasarar lashe zaɓe to za ta karɓe dukkan wuraren da gwamnati mai ci ta siyar.

Ya kuma nuna takaicinsa kan yadda ya ce, gwamnatin Kano ta gaza kafa kwamitin binciken waɗanda ƴan sandan SARS suka ci zarafi domin bi musu haƙƙinsu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!