Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kowane Gauta

Mun gama tattaunawa da Obaseki kan batun dawowarsa APC – Shehu Isa Driver

Published

on

Mun gama tattaunawa da zababban gwamnan Edo God win Obaseki kan batun dawowarsa APC nan gaba kadan.

Mataimaki na musamman ga gwamna Ganduje Shehu Isa Driver yace dolene a yabawa gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje dangane da zaben da aka gudanar a zaben Edo ganin yadda akayi lafiya aka gama lafiya.

Shehu Isa ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Kowane Gauta na gidan Radio Freedom, yana mai cewa yadda aka gudanar da zaben Edo cikin kwanciyar hankali da lumana abun alfahari ne a wajen al’umma wanda hakan yasa kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka yaba masa kan hakan.

Shuhu Isa Driver ya kara da cewa ‘yan kwankwasiyya su daina murnar lashe zaben Edo domin nan gaba kadan gwamnan jihar ta Edo zai dawo jam’iyyar sa ta APC domin sama sun kammala komai da shi.

Abun takaici ne a dinga amfani da Ganduje wajen yin murdiyar zabe – Bashir Sanata

Kowane Gauta: Tsarin karba-karba ya zama tsohon yayi a PDP inji Sule Lamido

Hon Musa Ilyasu kwankwaso ya kalubalanci ‘yan kwankwasiyya dasu daina murnar lashe zaben gwamnan jihar Edo kasan.

Hon Musa Ilyasu kwankwaso ya bayyana hakane ta cikin shirin Kowne Gauta, yana mai cewa ‘yan kwankwasiyya su dai na murnar lashe zaben a yanzu domin zaben Ondo yana nan.

Yace kowa yasan duk irin ruba da kwankwasawa keyi saboda samun nasarar da gwamnan ya samu, amma sujira a kammala zaben Ondo.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!