Kowane Gauta
Siyasar Kano : Yusuf Zara ya yi kakkausar suka ga Ganduje kan ciyo bashi a China
Yusuf Mai Kano Zara Kofar Na’isa daga jam’iyyar PDP a Kano ya yi kakkausar suka kan shirin Gwamnatin jihar Kano na karbo bashi daga kasar China.
Yusuf Zara ya bayyana haka ne ta cikin shirin Kowane Gauta na nan tashar Freedom Radio wanda sashi na talatin da tara da ya bada damar fadin albarkacin baki na kasar nan.
Mai Kano Zara ya ce ba dai dai bane a ciyowa al’ummar jihar Kano bashin da za’a dauki sama sa shekaru hamsin a na biyansa batare da an nemi amincewar mutanan Kano ba.
Yusuf Zara yace kamata yayi Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya nemi shawarar masana kasancewar bashin da yake niyyar karbowa a China yana dauke da kudin ruwa kuma yin hakan yasabawa addinin musulunci.
You must be logged in to post a comment Login