Labarai
Rundunar Soji ta hallaka dan ta’adda tare da kubutar da wadanda aka sace

Rundunar soji ta Operation Hadin Kai ta halaka wani dan ta’adda tare da ceto wasu da aka sace, yayin wani farmaki da suka kai maboyar ’yan ta’addan a jihar Borno.
Wannan na cikin sanarwar da Jami’in Yada Labarai, Laftanar Kanal Sani Uba, ya fitar a ranar 4 ga Yuni 2026.
Ya ce, dakarun sun kai hare-hare yankin Wulgo, inda aka gano maɓoyar ’yan ta’adda tare da lalata wasu daga cikin kayan aikin su.
Sanarwar ta ce, an ceto wasu da aka yi garkuwa da su, yayin da wasu ’yan ta’adda suka tsere sakamakon artabu da dakarun rundunar.
Rundunar ta ce za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta domin murkushe ayyukan ta’addanci da yankin Arewa maso Gabas.
You must be logged in to post a comment Login