Connect with us

Labarai

Sojoji sun daƙile hare-haren ‘ƴan ta’adda’ a Arewa maso Gabasin Najeriya

Published

on

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation HADIN KAI sun samu nasarar daƙile wani yunkurin kutsen ‘’yan ta’adda’ tare da lalata hanyoyin samar musu da kayan aiki a yankin Arewa maso Gabashin kasar.

Wannan na daga cikin kokarin da rundunar ke yi na kakkabe karfin ’yan ta’adda da hana su ci gaba da kai hare-hare.

A Jihar Borno, sojoji sun yi gaggawar mayar da martani bayan hangen motsin ’yan ta’adda da ke kokarin isa cibiyar horas da sojoji a Buni Yadi a ranar 9 ga watan Yuni in ji sanarwar da rundunar ta fitar.

Rundunar ta ce sojojinta sun bude wa maharan wuta inda suka fatattaki su tare da kashe wasu daga cikinsu, inda aka gano gawar ‘yan ta’adda biyu da kuma babur daya a wurin.

A wani bangare kuma, farmakin sirri da aka gudanar ya kai ga kama wasu da ake zargi suna samar wa ’yan Boko Haram da ISWAP kayan aiki a yankin Damboa.

Rundunar sojin ta jaddada cewa wadannan nasarori na nuna yadda take da kudurin karya hanyoyin taimaka wa ’yan ta’adda tare da tabbatar da tsaro da dawowar zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!