Labarai
Sojoji sun gano masana’antar kera makamai a Nasarawa

Rundunar sojin Najeriya, ta ce, dakaruna na Operation WHIRL STROKE, sun gano wata masana’antar ƙera makamai ba bisa ƙa’ida ba da ke ɓoye a yankin Agwatashi da ke ƙaramar hukumar Doma a jihar Nasarawa.
Rundunar, ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X.
Rahotanni sun nuna cewa wurin an ɓoye shi ne domin ƙera makaman da ake bai wa masu aikata laifuka a yankin da ma wajen sa.
Kwamandan rundunar, Manjo Janar Moses Gara ya buƙaci sojojin su da su ci gaba da dogaro da sahihan bayanan sirri domin tarwatsa cibiyoyin aikata laifuka.
You must be logged in to post a comment Login