Labarai
Babbar Jojin Najeriya ta gargaɗi alƙalai da lauyoyi game da gudanar da shari’o’in Siyasa

Babbar Jojin Najeriya mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta gargaɗi alƙalai da lauyoyi da su yi riko da gaskiya da riƙon amana wajen gudanar da shari’o’in siyasa, yayin da ƙasar ke shirin babban zaɓen shekarar 2027.
Ta bayyana haka ne a yau Litinin, yayin buɗe shekarar shari’a ta 2026 zuwa 2027 a harabar Kotun Ƙoli da ke birnin tarayya Abuja, inda ta ce dole ne kotuna su yi adalci tare da bin doka wajen yanke hukunci kan rigingimun zaɓe.
Kudirat Kekere-Ekun ta ce alƙalai su guji duk wani abu da zai sa a yi zargin suna goyon bayan wata jam’iyya ko ɗan takara, domin ayyukansu da kalamansu za su kasance ƙarƙashin kulawar jama’a.
Ta kuma yi gargaɗi kan neman kai ƙara kotunan da ake ganin za su fifita wani ɓangare, ko shigar da ƙararraki daban-daban kan abu ɗaya, tana mai cewa hakan na iya kawo cikas ga gudanar da adalci.
Haka kuma, ta buƙaci lauyoyi su nuna ƙwarewa da kulawa wajen shigar da ƙarar da ta shafi siyasa da zaɓe, musamman idan ana gudanar da makamanciyar shari’a a wata kotun.
You must be logged in to post a comment Login