Connect with us

Labarai

Sojoji sun kubutar da mutane 15 da aka yi garguwa da su

Published

on

Rundunar Sojin kasar nan, ta ce dakarunta sun ceto mutane 15 da aka yi garkuwa da su, tare da kama wasu mutane biyu da ake zargi da aikata garkuwa da mutane, a wasu hare-haren da ta gudanar a jihohin Edo, Kaduna, Benue, Kogi da Plateau.

 

Rundunar ta ce dakarunta sun gudanar ayyukan ne a ranakun 1 da 2 ga Oktoban da muke ciki, bayan wani samame da sintiri a wasu wurare da ake zargin ‘yan bindiga na fakewa.

 

A jihar Edo, dakarun Bataliya ta 195 sun ceto wasu mutane uku bayan da suka mayar da martani ga rahoton sace mutane da aka kai musu a hanyar Ekor zuwa Ikakumo, a karamar hukumar Akoko-Edo.

 

Rundunar ta ce sauran ayyukan da aka gudanar a jihohin Kaduna, Benue, Kogi da Plateau sun taimaka wajen ceto wasu mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma cafke wasu daga cikin wadanda ake zargi da hannu a ayyukan ta’addanci.

 

Rundunar Sojin ta ce dakarunta za su ci gaba da gudanar da samame da sintiri domin tabbatar da tsaron al’ummomi da kuma dakile ayyukan masu garkuwa da mutane.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!