Connect with us

Labarai

Gwamnonin Arewa Maso Gabas sun amince da kafa tsarin sufuri ta jiragen sama

Published

on

Gwamnonin jihohi shida na Arewa maso Gabashin Najeriya sun amince da kafa tsarin jigilar fasinjoji da kayayyaki ta jiragen sama.

 

Sanarwar da shugaban ƙungiyar gwamnonin yankin, kuma gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya sanya wa hannu bayan taronsu karo na 13 a Maiduguri, ta ce matakan za su taimaka wajen rage kuɗin sufuri da bunƙasa tattalin arziki. Haka kuma, gwamnonin sun yi maraba da shirin samar da babura masu kafa uku 10,000, bas-bas 10 da motocin haya 300 masu amfani da wutar lantarki.

 

A ɓangaren tsaro da ilimi, gwamnonin sun yaba da ƙoƙarin jami’an tsaro wajen yaƙi da ta’addanci, tare da buƙatar ƙarfafa musayar bayanan sirri da haɗin gwiwa tsakanin jihohi. Sun kuma yi kira da a ƙara zuba jari a ilimi, samar da ayyukan yi ga matasa da kuma kammala manyan ayyukan more rayuwa a yankin.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!