Labarai
Gwamna Zulum ya musanta hannu a kama ‘yan adawa

Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya musanta cewa ya bayar da umarnin kama wasu magoya bayan jam’iyyun adawa ko mutanen da ke sukar gwamnatin sa.
Gwamnan ya ce ba shi da masaniya kan kamen wasu mutane da ake zargin jami’an ’yan sanda sun tsare su a Maiduguri, bisa zargin sanya rigunan da ke dauke da rubutun “Tinubu Must Go”.
Zulum ya bayyana cewa shi bai bayar da umarnin kama mutanen ba, inda ya ce gwamnatinsa ta fi mayar da hankali ne kan tabbatar da zaman lafiya da sake gina jihar Borno bayan shekaru ta na fuskantar hare-haren Boko Haram.
Ya ce ba shi da dalilin jin tsoron jam’iyyun adawa, domin jihar Borno ta kasance karkashin jam’iyyar APC tsawon shekaru, kuma abin da ya fi muhimmanci a gare shi shi ne inganta rayuwar al’ummar jihar.
You must be logged in to post a comment Login