Connect with us

Labarai

NNPCL ya ce ragin kudin mai zai fara daga 1 zuwa 31 ga Oktober

Published

on

Kamfanin mai na kasa NNPCL ya bayyana cewa rangwamen naira 66 a kowace litar fetur da ya fara ranar 1 ga Oktoba zai ci gaba har zuwa ranar 31 ga Oktoba, 2026, a gidajen mai na NNPC a faɗin Najeriya.

 

A sanarwar da Shugaban Sashen Sadarwa na kamfanin, Andy Odeh, ya fitar yau Juma’a, NNPC ta ce an fara rangwamen ne domin bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai, kuma ba dawo da tallafin fetur ba ne.

 

Kamfanin ya fayyace cewa rangwamen ya shafi gidajen mai na NNPC  kaɗai, kuma bai kafa farashin fetur iri ɗaya a ƙasar ba ko sauya tsarin farashin da kasuwa ke ƙayyadewa, inda kamfanin ya buƙaci jama’a su yi watsi da fassarar cewa an dawo da tallafin fetur. 

 

NNPCL ta kuma jaddada aniyar ta, ta tabbatar da wadatar mai da haɗa kai da gwamnati domin rage nauyin tsadar mai ga iyalai da ’yan kasuwa.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!