Labarai
Sojojin Najeriya sun isa kasar Saudiya don gudanar da atisayen soja
A jiya Talata, kakakin rundunar sojan kasar Masar ya bayar da sanarwar, sojojin ruwan kasar sun isa kasar Saudiyya, domin hadin gwiwa da takwarorinsu na kasashen Saudiyya, da Jordan, da Yemen, da Djibouti da kuma Sudan, wajen gudanar da atisayen soja.
Sanarwar ta ce, burin da ake neman cimmawa a wannan atisayen soja shi ne, inganta kwarewar sojojin wajen gudanar da yaki na hadin gwiwa a kan teku.
Rundunar sojojin Masar na kokarin bunkasa hulda da takwarorinta na kasashen da abin ya shafa, ta yadda za su tinkari kalubalen da suke fuskanta, da ma kiyaye tsaro da zaman lafiyar a shiyyar, kuma wannan atisayen soja wani mataki ne da aka dauka domin cimma wannan buri. A cikin kusan shekara daya da ta gabata, Masar ta hada kan kasashen Amurka, da Faransa, da Ingila, da Italiya, da hadaddiyar daular Larabawa, da Bahrain da kuma Kuwait, wajen gudanar da atisayen soja, atisayen da ya shafi rundunar sojin ta ta kasa da ruwa da kuma ta sama