Kiwon Lafiya
SOKOTO:Asibitin koyarwa na jami’ar Usman Danfodiyo sun fara tiyatar zuciya
Asibitin koyarwa na jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto ya fara gudanar da tiyatar zuciya, ga marasa lafiya da ke fama da lalurar.
Shugaban asibitin Dr. Nasir Muhammed ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai jiya a garin Sokoto.
Ya ce ya zuwa yanzu akwai kididdigar mutane sama da dubu biyar da suke bukatar tiyatar zuciya a jihohin Sokoto da Kebbi da kuma Zamfara.
Dr. Nasir Muhammed, ya kuma ce, sai dai abin damuwar shine mafi yawa na mutanen da ke bukatar tiyatar zuciyar talakawa ne da ba za su iya biyan kudin aiki ba.
A cewar shugaban Asibitin koyarwa na jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto, Asibiti daya na kusa-kusa da ke gudanar da tiyatar zuciya a wannan yankin, shine Asibitin Nizamiyya da ke Abuja, kuma suna karbar akalla naira miliyan biyar, ga duk majinyaci