Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Rahoto: Abin da binciken masana ya gano ga me da ciwon zuciya

Published

on

Binciken masana harkokin lafiya ya gano cewa ciwon zuciya ba iya baƙin ciki da ɓacin rai ne kaɗai ke haddasa shi ba.

A cewar su ana iya haifar jariri da ciwon zuciya.

Bincikin ya gano cewa kaso 30 cikin ɗari na mutane masu fama da ciwon zuciya na mutuwa ne sanadiyyar cutar.

Hakan dai na zuwa ne adaidai lokacin da ake gudanar da bikin ranar tunawa da masu fama da ciwon zuciya ta duniya a yau, wanda majalisar ɗinkin duniya ta ware duk ranar 29 ga watan Satumbar kowacce shekara.

Kungiyar lafiya ta duniya WHO ce ta amince da ranar 29 ga satumbar ko kowacce shekara don ta zamo ranar tunawa da masu dauke da ziwon zuciya a fadin duniya.

An ware ranar domin samo hanyoyin kariya da kuma magance ciwon zuciya a tsakanin al’umma.

Masanan sun ce cikin abubuwan da suke haifar da ciwon zuciya sun haɗa da rashin motsa jiki, da shan taba sigari da shan giya.

Kazalika shan magani ba bisa ka’ida ba musamman ga mata masu dauke da juna biyu su kan haifi jariri da ciwon zuciya.

Sai dai binciken masana harkar lafiya ya nuna cewa anan jihar kano masu dauke da ciwon zuciya yawan su na kara karuwa, lamarin da ke janyo asarar rayuka.

Kamar yadda Dakta Jamil Ismail Ahmad ƙwararren likitan tiyatar zuciya da kirji ne a asibitin koyarwa na Aminu Kano ya bayyana.

Sai dai ya ce, za a iya kaucewa kamu da matsalar ta hanyar daina mu’amala da ƙwayoyin maye, da kuma sanyawa zuciya abubuwan nishaɗi da kuma yawan motsa jiki da rage cin kitse.

Sai dai bikin ranar tunawa da masu fama da ciown zuciya ya zo ne adaidai lokacin da likitoci masu neman ƙwarewa ke tsaka da yajin aiki na sama da watanni biyu lamarin da ke barazana ga harkokin lafiya.

A bana dai an yiwa bikin ranar tunawa da masu cizon zuciya take da “wayar da kai tare da daukan matakan kare kai daga kamuwa da ciwon zuciya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!