Jigawa
Son zuciya ne yasa aka samar da Inconculusive – Garba Ɗantiye
Tsohon dan Majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Garki da Ɓabura a jihar Jigawa Nasiru Garba Ɗantiye, yace son zuciya ne ya sa aka samar da tsarin Inconclusive a kasar nan.
Nasir Garba Ɗantiye ya bayyana hakan ne a zantawar sa da Freedom Radio.Ya ce duk Ƙasar da ta samu cigaba to harkokin zaben Ƙasar ana gudanar da shi cikin gaskiya da adalci,
“a baya munga yadda aka gudanar da wani sabon tsarin mai suna Inconclusive, wanda a doka bamu san shiba ƙirƙirsa kawai a kai,”
duk zaɓen da akai aka bayyana shi a matsayin Inconclusive to zakaga son zuciya na biyu baya domin babu shi kuma bamu san shi a doka ba,”
“A ƙasar nan muna da hukumar zabe mai zaman kanta INEC, sai dai duk gwamnatin da ke shugabancin wannan lokacin to fa itace ke gudanar da ita,
shiyasa muke cewa ba za’a taba samun zabe mai inganci ba muddin hukumar bata samu damar ikwan gudanarwa da kanta ba,”
“Muna ganin yadda a wasu guraren ake samun wasu da suke kada kuri’u ciki harda kananan yara, kuma kowa ya san da hakan gwamnatoci da hukamar zaɓe suna gani amma babu wani mataki da suke iya ɗauka ,”
“A irin haka ne fa ake gudanar da wani abu wai shi Inconclusive wanda jami’iyyar da ba sune ke da mulki ba idan sun ci zabe sai a ki fada hakan ne yasa ake samun zaɓen mara inganci ,”
“Lokacin tsohon shugaban hukumar Farfesa Attahiru Jega ne aka samar da wata na’ura da zata rika tantance masu zaɓe, da shugaba Muhammad Buhari da ‘yan majalisu duka sun samu nasara a lokacin
Tsohon ɗan majalisar Nasir Garba Ɗantiye ya ce idan har anaso ‘yan Ƙasa su gamsu da irin zaɓen da ake gudanarwa to kawai a kirga kuri’u a inda aka gudanar da zaben.
Haka zalika ya ce sabuwar hanyar gudunar da zabe ta hanyar kafar Sada zumunta zata tsaftace yadda zabuka a ƙasar nan zasu inganta.
You must be logged in to post a comment Login