Connect with us

Labarai

SSANU da NASU za su dakatar da yajin aiki daga 11 ga Mayu

Published

on

Kungiyoyin ma’aikatan jami’o’i da ba malamai ba, wato NASU da SSANU, sun sanar da dakatar da yajin aikin da suke yi a fadin kasar nan daga ranar Litinin, 11 ga watan Mayu, 2026, bayan cimma sabuwar yarjejeniya da gwamnatin tarayya.

Sanarwar ta fito ne ta hannun kwamitin hadin gwiwa na kungiyoyin biyu (JAC), inda suka bayyana cewa sun dauki wannan mataki ne bayan jerin ganawa da suka yi da kwamitin sake duba yarjejeniyar albashi na gwamnati karkashin jagorancin Yayale Ahmed. Kungiyoyin sun ce sun amince da dakatar da yajin aikin ne bayan gwamnati ta nuna kudirin kammala tattaunawar da ke gudana cikin gaggawa.

A cewar shugabannin kungiyoyin, daya daga cikin muhimman batutuwan da aka tattauna shi ne batun karin kashi 30 cikin 100 na albashi a karkashin tsarin CONTISS, wanda a baya aka gabatar amma daga baya aka janye. Sun bayyana cewa gwamnati ta yi alkawarin sake duba wannan batu tare da gabatar da sabon tsari mai gamsarwa.

Kungiyoyin NASU da SSANU sun shiga yajin aikin ne a ranar 1 ga Mayu saboda jinkirin da aka samu wajen kammala yarjejeniyar albashi da kuma rashin gabatar da sabbin shawarwari daga bangaren gwamnati. Sun ce wannan jinkiri ne ya tilasta musu daukar matakin yajin aiki domin neman hakkokinsu.

Sai dai a sabon matsayar da aka cimma, gwamnatin tarayya ta yi alkawarin kammala duk wata tattaunawa da ta rage cikin makonni biyu bayan dakatar da yajin aikin. Haka kuma, kungiyoyin sun umarci rassansu a duk fadin kasa da su gudanar da taruka domin sanar da mambobinsu wannan sabon ci gaba tare da shirin komawa bakin aiki.

Kungiyoyin sun kuma yabawa mambobinsu bisa hadin kai da goyon bayan da suka bayar yayin yajin aikin, tare da bayyana fatan cewa gwamnati za ta cika alkawurran da ta dauka domin kauce wa sake barkewar irin wannan matsala a nan gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!