Kiwon Lafiya
Sufeto janar Yan Sanda ya ki amincewa da wata sikirar kudirin gyaran dokar rundunar
Sufeto janar na ‘yan sandan kasar nan Ibrahim Idris, ya ki amincewa da wata sikirar kudirin gyarar dokar rundunar ‘yan sandan kasar nan da majalisar dattawa ta bukata wanda ke neman majalisun dokokin tarayyar kasar nan su rika tantance duk wanda za a nada a matsayin sufeto janar na ‘yan sanda.
Ya ce matukar lamarin ya fada hannun majalisun dokokin tarayyar kasar nan to kuwa ba ko shakka zai kawo nakaso ga ayyukan ‘yan sanda a kasar nan.
Ibrahim Idris ya kuma ce idan hurumin ya fada hannun ‘yan majalisun tarayya to kuwa za su rika amfani da damar da suke da ita wajen biyan bukata na siyasa.
Sufeto janar na ‘yan sandan ya bayyana hakan ne a jiya, yayin taron jin ra’ayi kan kudirin dokar sabunta ayyukan ‘yan sanda.
A don haka sufeto janar na ‘yan sandan ya bukaci da a cire bangaren da ke neman sahalewar majalisun dokokin tarayyar kasar nan kafin nada shugaban na ‘yan sanda.