Labaran Kano
Sulhu tsakanin al’umma zai rage cunkoso a kotuna
Wata kungiya mai rajin ganin an tabbatar da gaskiya da adalci dake garin Kumbotso, ta ce samar da kungiyoyin al’umma da zasu dinga aikin sulhunta jama’a zai taimaka wajen rage yawan yadda ake shigar da kararraki gaban jami’an tsaro da ma masu unguwanni a jihar Kano.
Shugaban kungiyar Isyaku Ahmad ne ya bayyana hakan ta bakin sakataran kungiyar dake kula da tsare-tsare Iliyasu Nuhu, yayin taron jin ra’ayin jama’ar garin na Kumbotso kan ayyukan da kungiyar ta sanya a gaba.
Ilyasu Nuhu ya ce a yanzu ana yawan samun shigar da kararraki gaban jamian tsaro kan dan abinda za’a a iya magance shi ta hanyar sulhu, amma sai batun ya yi zafin da har sai anje gaban kotu, yana mai cewa hakan na taka rawa wajen samar da cunkoso a gaban kotuna.
Wasu daga cikin mahalartar taron sun bayyana cewa wannan sabon tsarin zai taka rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kuma fahimtar juna tsakanin al’ummar yankin.
Wakilin mu Abubakar Tijjani Rabi’u ya ruwaito cewa taron ya samu halartar shugabannin addinai daban-daban da kungyoyin kare hakkin dan adam dana yaki da cin hanci da rashawa da sauran al’umma.