Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sunday Igboho na da alaƙa da Boko Haram – Abubakar Malami

Published

on

Gwamnatin tarayya ta gano masu daukar nauyin jagoran tsagerun Yarabawa Sunday Igboho.

A cewar gwamnatin yana da alaƙa da masu daukar nauyin ƴan ƙungiyar Boko Haram.

Ministan shari’a kuma atoni janar na tarayya Abubakar Malami ne ya tabbatar da hakan yayin taron manema labarai a Abuja.

Abubakar Malami ya ce bincikensu ya gano yadda aka tura wa Sunday Igboho kuɗi sama da naira miliyan 127 ta asusun banki 43 cikin bankuna 9.

Ministan ya kara da sun gano cewa Sunday Igboho yana da alaƙa da mutumin nan da aka yanke wa hukuncin ɗaurin rai-rai a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa Surajo Abubakar Muhammad, sakamakon samunsa da laifin daukar nauyin kungiyar Boko Haram.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!