Labaran Wasanni
Super Eagles za ta buga wasa da Jamhuriyar Afrika ta tsakiya ba tare da manyan ‘yan wasan ta 3 ba
Kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles zata fafata da kasar Afrika ta tsakiya a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya na shekarar 2022 a kasar Qatar.
Karawar da zata gudana a filin wasa na Teslim Balogun dake jihar Lagos a yau Alhamis 07 ga Oktoban shekarar 2021 da misalin karfe biyar na yamma.
Najeriya dai itace ke jagorantar rukunin C da maki shida bayan doke kasashen Liberia daci 2-0 da kuma Cape Verde daci 2-1.
Wannnan karawar dai itace ta farko tsakanin kasashen biyu a wasan kasa da kasa da zasu fafata a wasan na share fage.
Sai dai tawagar Super Eagles karkashin jagorancin Gernot Rohr zata buga wasan ba tare da manyan ‘yan wasanta uku ba Oghenekaro Etebo, Wilfred Ndidi da kuma Alex Iwobi sakamakon jinyar raunin da suke fama da ita.
Mai horar da kungiyar dan kasar Jamus na shirin yin amfani da Victor Osimhen ko Paul Onuachu ko kuma Kelechi Iheanacho domin zurawa tawagar kwallo.
Haka zalika tawagar ta kasar Afrika ta tsakiya zata buga wasanta ba tare da dan wasa Geoffrey Kondogbia ba.
You must be logged in to post a comment Login