Labarai
Tabar wiwi ta yi sanadiyar daurin rai-da-rai ga wani matashi
Kotu ta yi hukuncin daurin rai-da-rai ga dan shekara 24 sakamakon safarar tabar wiwi
A cewar alkalin kotun idan har ba a daukar irin wadannan tsauraran matakai kan masu safarar kwayoyi zai yi matukar wuya a dakile matsalar shaye-shaye a kasar nan.
Wata babbar kotun tarayya da ke Ibadan a jihar Oyo ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai ga wani matashi dan shekaru 24 mai suna Sodiq Ramon sakamakon kama shi da laifin safarar miyagun kwayoyi.
Kotun ta kama Sodiq Ramon da laifin safarar tabar wiwi mai nauyin kilo 57.2.
Da ta ke sanar da hukuncin mai shari’a Joyce Abdulmaleek, ta ce, ta yanke hukunci ne ga Sodiq Ramon saboda ta gamsu da kwararan hujjoji da aka gabatar akan shi.
‘‘Hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta gabatar da kwararan hujjoji gaban kotu da suka daura alhakin safarar tabar wiwin kan Sodiq Ramon,’’ a cewar alkalin.
You must be logged in to post a comment Login