Labarai
Taimaka wa manoma da gwamnatin ke shirin yi zai kawo gagarumin sauyi- AFAN

Shugaban Kungiyar gamayyar Manoma ta Najeriya AFAN Alhaji Muhammad Magaji Gettado, ya ce, matakin da gwamnatin tarayya ke shirin dauka na tallafawa manoman rani da na damuna zai kawo gagarumin sauyi wajen wadata kasar nan da abinci a damunar bana.
Alhaji Muhammad Magaji Gettado ya bayyana hakan yayin kaddamar da shirin tallafin mai suna FarmerMoni ga shugabannin manoman jihohi talatin da shida dake kasar nan, da aka gudanar a ranar Laraba.
Alhaji Muhammad Magaji Gettado ya kara da cewa wannan wani tagomashi ne ga manoma da masu kiwon dabbobi, yayin da suke shirin tunkarar noman rani da na damuna.
Shugaban ya tabbatar da cewa kungiyar ta AFAN za ta sa ido kan tantancewar domin ganin manoma na gaskiya ne kawai zasu ci gajiyar tallafin.
You must be logged in to post a comment Login