Manyan Labarai
Taimakawa almajairai lokacin sanyi taimakon kai- DR, Hadiza Kere
Daga Nasiru Salisu Zango
Sakamakon shigowar muku mukun sanyi galiban mutane kan dauki matakan samar da dumi ga iyalansu ta hanyar tanadar barguna da sauran ababan tserar da kai daga farmakin hunturu musamman ma na wannan shekarar wanda ake cewar ba a taba ganin irinsa ba,
Sai dai kuma ba kowa ne ke iya tunawa da almajirai da sauran yara dake gararamba a gari ba.
Irin wadannan yara sanyin kan kare akansu babu kyakyawan wurin kwana balle abin dumama makwanci, wannan ne ya ja hankalin wasu bayin Allah da suka hada da Dr Hadiza Kere Abdurrahman dake karatu a ingila da hadin gwiwar wasu ma su tausayi da su ka hada da Tani Ester da Abubakar Widi Jalo.
Yayind a suka mayar da hankali wajen samar da hanyoyin samun sauki ga almajirai da sauran yaran da ke gararamba a gari, sun kuma girka gidauniyar neman taimako wacce ta ja hankalin al’umma su ka fara tattara kudi
Ka zalika ya zuwa yanzu an sayi barguna da safuna masu tarin yawa an kuma rarraba ga tsangayu da kuma wuraren da irin wadannan yara ke fakewa,na tambayi Abubakar Widi jalo ko me ya ja hankalinsu akan wannan aiki.
Sai ya ce ya zama wajibi kasancewar duk wanda ya taimaki wani Allah zai taimaka masa.
Ita ma Tani Ester ta yi mana Karin haske kan yadda addinin muslunci ke karfafa gwiwar mutane su taimaki juna.
Sai dai a matsayin ta na uwa ta ja hankali kan muhimmancin iyaye su dauki nauyin ‘ya’yansu maimakon sakinsu suna gararamba a gari har am ana tunanin yadda za a taimaka musu
Yanzu haka dai wadannan bayin Allah na cigaba da tattara tallafi domin cigaba da fadada wannan aikin alheri.