Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tarihin marigayi Dan Iyan Kano Yusuf Bayero

Published

on

An haifi marigayi Dan Iyan Kano Yusuf Bayero a shekarar 1933, ya halarci makarantar Elementary ta Kofar Kudu.

Marigayi Alhaji Yusuf Bayero ya kasance mamba a majalisar wakilan arewacin kasar nan, ya kuma zama sakataren gudanarwar jihar Kaduna, sannan ya dawo jihar Kano bayan juyin mulkin soji da akayi a shekarar 1966.

Haka zalika an nada shi sarautar Dan ruwatan Kano kuma hakimin Ajingi na farko.

Gwamnatin Kano ta wancan lokaci ta marigayi Alhaji Muhammad Abubakar Rimi ta saukeshi daga Dan Ruwatan Kano Hakimin Ajingi a shekarar 1981.

Saidai Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya sake nada shi sarautar Dan Ruwatan Kano kuma hakimin karamar hukumar Bichi a shekarar 1983.

Sannan an daga likkafarsa zuwa Danburan da Barden Kano lokacin da yake hakimin Bichi.

Karin labarai:

Fadar shugaban kasa ta kaiwa Sarkin Kano ziyarar ta’aziyya

Yanzu-yanzu: Yar Sarkin Kano Sanusi na daya ta rasu

Haka kuma an daga likkafarsa zuwa sarautar Dan Iyan Kano a shekarar 1993 inda akayi masa sauyin aiki zuwa Dawakin Kudu.

Ranar 20 ga watan August na shekarar 2019 ne masarautar Gaya ta sauke shi daga sarautar Dan Iyan Kano hakimin Dawakin Kudu bayan da gwamnatin Kano tayi dokar karin masarautu a jihar.

Dan Iyan Kano Yusuf Bayero ya rasu a ranar Asabar 09 ga watan Mayu na shekara ta 2020.

Anyi jana’izarsa a safiyar Lahadi 10 ga watan Mayu na shekarar 2020, kamar yadda addinin musulunci ya tanada a fadar sarkin Kano.

Marigayi Alhaji Yusuf Bayero kani ne ga marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, kuma shi ne cikon mutane biyu da suka rage acikin ‘ya’yan sarki Abdullahi Bayero, yanzu saura guda daya Kenan.

Marigayi Dan Iyan Kano Alhaji Yusuf Bayero

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!