Addini
Tarihin zikirin shekara da ake yi a fadar sarkin Kano
Zikirin shekara dai taron addu’a ne da mabiya darikar Tijjaniyya suke gabatarwa kowace shekara, domin addu’o’in zaman lafiya da cigaba ga al’ummar musulmai, wanda ake yi a fadar maimartaba sarkin Kano, taron ya samo asali ne a shekarar 1999AD, lokacin da gwamnatin jihar Kano ta waccan lokacin karkashin gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso ta shirya bikin cikar garin Kano shekaru dubu (1000) da kafuwa.
A shekarar ta 1999AD dai ta dace da shekara 100 cif da shigar darikar ta tijjaniyya masarautar Kano.
Dangane da cikar garin Kanon shekaru dubu 1000 ne masarautar Kano karkashin Maimartaba Alhaji. Dakta Ado Bayero a wancan lokaci ta shirya zikiri da addu’o’in ranar jumu’a, wanda ake gudanarwa har izuwa yanzu.
Mabiya darikar tijjaniyya daga sassa daban-daban na ciki da wajen kasar nan na halartar taron.
Tun bayan hawan maimartaba Sarkin Kano Mallam Muhammadu Sanusi II na biyu dai ya kawo sabon tsari na gabatar da addu’ar neman zaman lafiya wadda ake gabatarwa a kowacce jumu’a da safe a babban masallacin jumu’a na garin Kano.
A yau jumu’a 04 ga watan Oktoba ne dai ake gudanar da taron na bana, wanda ya samu halartar dubunnan al’umma da dama ciki harda Maimartaba Sarkin Kano Mallam Muhammadu Sanusi II, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Gwamna Nasir El-rufa’I na jihar Kaduna, ‘ya’yan Sheikh Ibrahim Inyass da kuma mataimakin Gwamnan jihar Kano Dakta Nasiru Yusuf Gawuna.