Ƙetare
Taron MDD: Rashin haɗin kai ne ya kawo rarrabuwar kawuna da juyin mulki a wasu ƙasashen – Antonio Guterres
Sakatare Janar na Majalisar ɗinkin duniya Antonio Guterres ya bayyana matukar damuwa akan yadda ake fuskantar rashin hadin kai tsakanin manyan kasashen duniya.
A cewar sa, wannan ne ya ke haifar da illa wajen zaman lafiyar da kuma shawo kan matsalolin tsaro da kula da lafiyar jama’a da kuma tattalin arziki.
Yayin bude taron Majalisar karo na 76 a birnin New York dake kasar Amurka, Guterres ya tsokaci akan juyin mulkin da ake samu a wasu kasashe da kuma tashe tashen hankula.
Sakataren yace sun ga yadda aka samu karuwar kwace mulki da karfin tuwo, inda yake cewa juyin mulkin soji ya dawo, yayin d
a rashin hadin kai tsakanin kasashen duniya baya taimakawa wajen tinkarar irin wadannan matsaloli.
Guterres yace rarrabuwar kawuna a shiyoyin duniya na illa ga hadin kan duniyar da kuma rage karfin kwamitin sulhu na daukar matakan da suka dace a lokacin da ake bukatar su, abinda ke taimakawa wajen baiwa shirin kama karya wurin zama.
Sakataren yace domin dawo da yarda da fata mai kyau a duniya, suna bukatar hadin kai ta hanyar tattaunawa da kuma fahimta.
Guterres yace suna bukatar zuba jari wajen kariya da aikin samar da zaman lafiya da kuma gina al’ummu tare da rage samar da makaman nukiliya, yayin da ya bukaci hadin kai wajen yaki da ta’addanci da kare hakkin Bil Adama tare da samar da wani sabon shiri na zaman lafiya.
Taron na bana ya samu halartar shugabannin kasashen duniya da dama sabanin yadda aka gani bara, yadda annobar korona ta hana shugabannin tafiya birnin New York.
You must be logged in to post a comment Login