Manyan Labarai
Tashar wutar lantarki a Mambila shaci fadi ne kawai – gwamnonin arewa maso gabas
Gwamnonin yankin arewa maso gabashin kasar nan sun ce aikin kafa tashar samar da wutar lantarki na Mambila shaci fadi ne kawai har yanzu, domin kuwa babu aikin a zahiri sai a takarda.
Tun da farko dai gwamnati ta tsara aikin tashar samar da wutar lantarkin ta Mambila mai karfin megawatt sama da dubu uku a kogin Dongo da ke kusa da kauyen Kakara a jihar Taraba ne.
A cikin wata takardar bayan taro da kungiyar gwamnonin ta fitar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, gwamnonin sun bukaci gwamnatin tarayya da ta mai da hankali wajen gudanar da aikin gadan-gadan.
A cewar takardar bayan taron matukar aka gudanar da aikin tashar samar da wutar lantarkin ta Mambila zai taimaka gaya wajen bunkasa tattalin arzikin kasar nan.
A bangare guda gwamnonin sun kuma bayyana cewa ba a yiwa yankin arewa maso gabashin kasar nan adalci ba musamman wajen manyan ayyukan raya kasa da gwamnatin tarayya ta sanya cikin kasafin kudinta na wannan shekara ba.
You must be logged in to post a comment Login