Kasuwanci
Tashin farashin dala ne musabbabin tsadar iskar gas – ƙungiya
ƙungiyar masu sayar da iskar gas anan Kano ta alakanta tashin farashin iskar gas da yadda darajar naira ke karyewa dala kuma ke ƙara tsada a wannan lokaci.
Alhaji Aminu Uba Waru ne ya bayyana hakan ta cikin shirin duniyar mu a yau na nan Freedom Radio.
“ƙarin farashin Dala da kuma na haraji da yake karuwa a koda yaushe shi ma na daya daga cikin abin da ke ƙarawa iskar gas din tsada”.
Alhaji Muhammad Omene wanda shi ne sakataran kungiyar masu sayar da iskar gas ta jihar Kano ya ce baya ga tashin farashin dalar, shigo da iskar gas din da ake daga kasashen Waje shima yana jawo tsadar sa.
“Tun a lokacin mulkin marigayi Abacha, kashi 70 cikin dari na iskar gas din da ake amfani da shi a kasar nan shigo da shi ake daga kasashen waje, sai dai a lokacin bai kai tsadar haka ba”.
“Kuma tsadar na da alaka da rashin aikin matatun man da ake da su a kasar nan musamman na Warri da Kaduna da kuma kalaba”.
Bakin sun bukaci mahukunta da su dauki matakin daya dace domin kawo karshen wannan matsalar
You must be logged in to post a comment Login