Labarai
Tawagar ECOWAS ta isa Guinea don sasanta rikicin juyin mulki
Tawagar kungiyar ECOWAS ta kasashen yammacin Afirka ta isa Guinea.
Ziyarar ta su za ta mayar da hankali domin tattaunawa da shugabannin sojojin kasar da suka yi juyin mulkin da ya kawo karshen gwamnatin tsohon shugaba Alpha Conde.
Ana sa ran tawagar ta ECOWAS za ta bukaci a mayar da mulki ga farar hula a kasar ta Guinea da kuma matsa kaimi kan bukatar gaggauta sakin tsohon shugaba Conde, wanda a yanzu ke tsare a hannun sojoji.
An tsare Conde, tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi masa a karkashin jagorancin Laftanar Kanal Mamady Doumbouya ranar Lahadi.
Sannu a hankali dai rayuwa a babban birnin kasar Conakry ta koma daidai a ranar Alhamis, inda aka sake bude kasuwanni, tare da ci gaban harkokin yau da kullum.
You must be logged in to post a comment Login