Connect with us

Labarai

Tawagar fadar shugaban ƙasa ta kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Marigayi Hamza Usman Darma

Published

on

Wata tawaga daga fadar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ta kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi fitaccen ɗan siyasa kuma dattijon ƙasa Alhaji Hamza Usman Darma, wanda Allah ya yi wa rasuwa kwanaki uku da suka gabata.

‎Tawagar ta ƙunshi mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin siyasa, Alhaji Kabir Masari, da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin da gwamnonin jihohin Yobe, Sokoto, Jigawa da Kano.

‎Da yake karanta saƙon ta’aziyyar Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ce, tawagar ta bayyana marigayi Hamza Darma a matsayin fitaccen ɗan siyasa wanda gudunmawar da ya bayar ga Kano da Najeriya ba za a manta da ita ba.

‎Da yake jawabi a madadin iyalan marigayin, Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya nuna matuƙar godiyarsa ga Shugaba Tinubu bisa alhini da ta’aziyyar da ya aiko ga iyalan marigayin dama al’ummar jihar Kano baki ɗaya game da wannan babban rashi na Alhaji Hamza Usman Darma.

‎Wakilin mu na gidan Gwamnatin kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa tawagar ta ƙunshi Gwamnoni da manyan ƴan siyasa da kwamishoni da masu baiwa gwamnan Kano shawara.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!