Labarai
Za mu iya faɗaɗa matatun Kano domin samar da ruwan Famfo a ko ina- Kwamishina

Gwamnatin jihar Kano, ta ce ta fara yunƙurin gudanar da aikin ruɓanya ayyukan matatun Ruwa da jihar ke da su domin tabbatar da cewa kowanne yanki na samun wadataccen kuma ingantaccen Ruwan Famfo.
Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli Ruwa da kuma sauyin yanayi Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ne ya bayyana hakan a ganawarsa da manema labarai.
Kwamishinan ya ce, da dama daga cikin matatun ruwan an gina su ne tun shekaru masu tsawo da suka gabata, amma yanzu haka gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf, ta gudanar da aikin gyara waɗanda suka daina aikin inda tuni wasu wuraren da suka shafe shekaru ba sa samun ruwan Famfo suka fara amfana da su, yayin da kuma ake ƙoƙarin ruɓanya ayyukan wasu manyan matatun nan ba da jimawa ba.
Kwamishinan, ya kuma bayyana cewa ba za zu zuba ido ko kuma saurara wa duk mutanen da aka samu da laifin gurɓata muhalli ko kuma sare bishiyu ba bisa ƙa’ida ba.
Kwamishinan ma’aikatar ta Muhalli, ruwa da kuma sauyin yanayi Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ya buƙaci al’umma da su riƙa kai musu rahoton duk masu gurɓata muhalli ko kuma sare bishiyu ba bisa ƙa’ida ba domin ɗaukar matakin da ya dace.
You must be logged in to post a comment Login