Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Thomas Tuchel ya saki matarsa Ƴar jarida bayan sun shafe shekaru 13 suna tare

Published

on

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Thomas Tuchel, ya sanar da raba gari da matarsa Mista Sisi Tuchel bayan da suka shafe shekaru 13 suna tare.

Mista Sissi wanda ta wallafa hotunan rabuwarsu da mijinta a karshen makon da ya gabata a shafikan sada zumunta.

‘Rabuwarmu ba abune mai dadi ba, sai dai babu yadda muka iya, wanda hakan shi ne masalaha a tsakanin mu’, a cewar Mista Sissi.

Watanni goma dai da suka ga bata, anga mista Sissi na zaune birnin Porto’s a filin wasa na Estadio do Dragao, kana daga bisani ta bi mijin nata zuwa kasar Ingila a lokacin da tawar Chelsea tayi nasara akan Manchester City a gasar cin kofin zakarun turai a kakar wasannin da ta gabata.

Zuwa yanzu dai Tuchel, na biyan kudin harajin fam miliyan 7 ako wacce shekara a Ingila, wanda kuma yanzu haka zai biya tsowur matarsa kudin yarjejeniyar auren da sukai.

Sissi Tuchel da Thomas Tuchel sunyi aure ne a shekarar 2009, da kawo yanzu suna da ‘ya’ya biyu a tsawon lokacin da suka shafe tare.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!